<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><title>Kamar Ruwa Ya Kan Sauko LW193</title>
<lyrics>[V1]
 1) Kamar ruwa ya kan sauko
 Bisa duniya busasshiya,
 Haka Ruhun Ubangiji
 Cikin can Ekklesiya,
 Sauko nan, ya Ruhun Allah,
 Sauko, muna kishinka. (2x)

[V2]
 2) Kamar raƃa ta kan faɗo
 Bisa ƙasa, ta kan tsaya,
 Ba ta fita, sai ta gama
 Nata aikin warkarwa.
 Sauko nan, ya Ruhun Allah,
 Sauko, muna jiranka. (2x)

[V3]
 3) Kamar wuta ta kan cinye
 Dauɗa, cuta, ruƃewa,
 Haka Ruhun Ubangiji,
 Zauna cikin zuciya.
 Kau da ƙarya, dukan lafi,
 Kone su da wutarka. (2x)

[V4]
 4) Aikin Ruhu mu ke roƙo,
 Ƴaƴansa na lafiya.
 Ƙaunar Ruhu mu ke nema,
 Ƙauna marar ƙarewa,
 Ba mu su, ya Ruhun Allah,
 Ba mu su, ba fasawa. (2x)</lyrics>
<hymn_number>193</hymn_number>
<author>Hughes, John (1873-1932), Williams, William (1717-1791)</author>
</song>